Kano ta sami jami’a ta farko mai zaman kanta

July 04, 2018

Kano ta sami jami’a ta farko mai zaman kanta

Hukumar kula da da jami’o’i na kasa ta mika wa sabuwar jami’a mai zamankanta ta farko a Jihar Kano.


Jami’ar mai suna Skyline University ta karbi shaidar amincewa ta fara aiki ne daga hukuma NUC ayu a Abuja.

Cikin Jami’o’i 75 masu zaman kan su dake kasar nan, kwaya biyu ne tal ke yankin Arewa Maso Yamma, da ya hada da Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, da Jigawa.

Al-Qalam dake Katsina da yanzu Skyline da za a bude a Kano mallakin Kamal Puri, wani dan kasar India.

Da yake mika shaidar amincewar ga shugaban Jami’ar Kamal Puri, dan kasar India, shugaban hukumar NUC Abubakar Rasheed ya ce jami’ar Skyline iat ce jami’a mai zaman ka an 75 da aka amince da a kasa Najeriya zuwa yanzu.

” Yanzu haka akwai jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya 42 a kasar nan sannan akwai 47 kuma mallakar gwamnatocin jihohi da 75 yanzu dake masu zaman kansu.
Premiumtimeshausa
Kano ta sami jami’a ta farko mai zaman kanta Kano ta sami jami’a ta farko mai zaman kanta Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

Wani matashi ya rataye kanshi saboda fitar da Argentina daga gasar cin kofin Duniya

July 04, 2018

Wani matashi ya rataye kanshi saboda fitar da Argentina daga gasar cin kofin Duniya

Bayan da kasar Faransa ta cire Argentina daga gasar cin kofin Duniya da ake bugawa a kasar Rasha, wani matashi a kasar Indiya, masoyin Messi ya shiga damuwa wadda har ta kaishi ga halaka kanshi.


Monotosh Halder dan kimanin shekaru 20 ya ki cin abinci a daren da aka cire Argentina, inda ya shige daki ya kulle, da safiya tafi aka kwankwasa daki shiru be budeba, sai aka kirawo 'yansanda.

Dole aka balle kofar dakin, aikuwa sai ga gawar halda na reto a rataye a saman dakin.

Mahaifinshi yace, dan nashi masoyin Argentinane, kuma tunda aka fara gasar cin kofin Duniya koda yaushe za'a buga wasa baya wuceshi, ya kara da cewa amma be yi tsammanin zai iya aikata haka ba, kamar yanda Goal suka ruwaito.
Wani matashi ya rataye kanshi saboda fitar da Argentina daga gasar cin kofin Duniya Wani matashi ya rataye kanshi saboda fitar da Argentina daga gasar cin kofin Duniya Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

Mutane na cewa na zama dan PDP saboda daukar hoto da Atiku>>Sheikh Ahmad Gumi

July 04, 2018

Mutane na cewa na zama dan PDP saboda daukar hoto da Atiku>>Sheikh Ahmad Gumi

Mun samu dubban ra'ayoyin jama'a bayan wallafa wani hoto da ke nuna fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya Dokta Ahmad Gumi tare da tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar a wurin wani daurin aure a Kaduna ranar Juma'a.


Dokta Gumi ya dade yana sukar wadansu manufofin gwamnati Shugaban kasar Muhammadu Buhari musamman lokacin tafsirinsa na azumin watan Ramadan na bana.

Atiku Abubakar, wanda ya koma jam'iyyar PDP a karshen bara, yana cikin wadanda suke neman shugaban kasar a zaben 2019.

Jama'a sun rika bayyana ra'ayoyinsu a shafukanmu na sada zumunta, inda wadansu suke ganin maganar da mutanen biyu suka yi a wurin daurin auren tana dangantaka da siyasa.

Akwai kuma wadanda suke ganin kamar malamin addinin yana kamun kafa ne a wurin tsohon mataimakin shugaban kasar.

Wannan ya sa muka tuntubi malamin ta waya, inda muka tambaye shi abin da ya fada wa Atikun lokacin da suka hadu a Kaduna.

"Bayan da muka yi gaishe-gaishe, na yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar bayanin cewa akwai wani daurin aure da muka hadu da ni da shi, aka dauki hotonmu da ni da shi da wani tsohon gwamna," in ji Dokta Gumi.

"Sai nake ba shi labarin mutane sun ce tun da an gan mu tare da ni da shi tare da wancan tsohon gwamnan, to na zama dan PDP. Al hali lokacin shi kansa dan APC ne."

Ya ce hakan yana nuna cewa "duk lokacin da aka gan shi da wani dan siyasa" sai wadansu mutane su rika yi musu mugun zato.

Har ila yau Dokta Gumi ya ce abu na uku da ya fada masa shi ne shi ba dan kowace jam'iyya ba ne, "ba na PDP, ba na APC."

Sai dai ya ce su ba za su iya yin shuru "idan muka ga za a cuci jama'a ko kuma za a taba addininmu ba."
bbchausa.
Mutane na cewa na zama dan PDP saboda daukar hoto da Atiku>>Sheikh Ahmad Gumi Mutane na cewa na zama dan PDP saboda daukar hoto da Atiku>>Sheikh Ahmad Gumi Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

Harry Kane yayi abinda Ronaldo, Messi da Neymar suka kasa yi a gasar cin kofin Duniya

July 04, 2018

Harry Kane yayi abinda Ronaldo, Messi da Neymar suka kasa yi a gasar cin kofin Duniya

A ci gaba da buga gasar cin kofin Duniya da akeyi a kasar Rasha, kasar ingila ta fitar da Colombia a wasan da suka kara na 'yan rukunin kasashe 16, tauraron dan kwallonta Harry Kane yaci kwallaye fiye da kowane dan kwallo a gasar ta cin kofin Duniya 2018.


Harry Kane nada kwallaye shida kenan zuwa yanzu wanda ya wuce Ronaldo dake da hudu da kuma Messi dake da daya wanda duka biyun tuni aka fitar da kasashensu daga gasar ta cin kofi Duniyar 2018, haka ma Kane ya wuce Neymar dake da kwallaye biyu.

Kane yaci kwallayen shidane a yumkuri tara kacal.

Yayin da shi kuma Ronaldo dake da kwallaye bakwai jumulla a gaba dayan gasar cin kofin Duniya daya taba bugawa, yaci kwallaye shidanshine a yunkuri saba'in da hudu.

Shi kuwa Messi me jimullar kwallaye shida a gaba dayan gasar cin kofin Duniya daya buga, yaci kwallayenshi shidane a yunkuri sittin da bakwai.

Shi kuwa Neymar sai da yayi yunkuri talatin da takwas sannan yaci jimullar kwallaye biyu da yake dasu a gasar cin kofin Duniya.

Koda yake dai wasu na sukar cewa baza'a taba hada kwallayen Kane din dana Ronaldo da Messi ba saboda yawanci da Fenareti yaci su amma dai zuwa yanzu shine a gabansu duk.
Harry Kane yayi abinda Ronaldo, Messi da Neymar suka kasa yi a gasar cin kofin Duniya Harry Kane yayi abinda Ronaldo, Messi da Neymar suka kasa yi a gasar cin kofin Duniya Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

Cikakken Sakon Tsohuwar Jaruma Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria

July 04, 2018
Ga Sakon Tsohuwar Jarumar Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria Ta Rubuta Wannan Sakon A Shafin Instagram Dinta
""Salam dear nigerians ,wasu suna amfani da sunana a face book sunamin karya iri iri da kuma bata suna a gareni Wanda ina kyautata zaton masoyan APC ne.hakan ya samo asaline domin sunsan bana shiri da boss dinsu Mr president.last week sun hada hotona Dana wani gardin banza a daji wai yana lalata dani sukaga hoton baiyi tasiri ba domin Allah ba azzalumin bawansa bane baya kuma kama bawa da laifin da bai aikata ba.to da suka ga hotona da suka hada da gardi Wanda kuke cewa timaya ne baiyi tasiri ba sai kuma suka dawo suka ce wai ni yar shi'A ce,shima suka ga baiyi tasiri ba da suka dangan tani da shi'A.sai kuma yau suka sake cewa wai na fita daga shi'A har na dawo ina addu'a Allah ya dauwa Mar da "sir zazzaky " a gidan yari .to karya ake min ni Sam banyi maganah akan sir zazzaky cewar Allah ya dauwa Mar dashi a gidan yari ba domin ni ina tsananin girmama sir zazzaky saboda sunansa daya Dana mahaifina kuma ni aduniya duk mai sunan mahaifina to ina daraji shi saboda duk mai sunan kallon uba nake masa a sakamakon kaunar da nakewa babana sosai.dan haka karya akemin .
Kuma ku masu son batamin suna ina son ku sani cewa annabi Muhammad s.a.w.yace :in duniya zata taru bata ISA ta daurawa bawa abunda Allah bai dauramasa ba na masifa ko alkairi haka kuma yace in da duniya zata taru bata ISA ta daukewa bawa abunda Allah ya daurawa bawansa na masifa ko alkairi.dan haka na dogara ga Allah kuma zai kare ni a bisa sharrin da kukemin iri iri akan buhari.sannan naji kunce na tuba wai na dena adawa da buhari ko ?to shima karya kukemin.ni yanzu ma na fara adawa dashi indai akan siyasa ne ,nagode.
daga ummi ibrahim(zeezee)""

Cikakken Sakon Tsohuwar Jaruma Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria Cikakken Sakon Tsohuwar Jaruma Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi

July 04, 2018

Rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta ce ta yi nasarar kubutar da mahaifin kyaftin din Super Eagles ta Najeriya, Mikel Obi, kwana uku bayan an sace shi.

Wata sanarwar da kakakin rundunar, SP Ebere Amaraizu, ya fitar ta ce da sanyin safiyar Litini ne jami'an 'yan sandan suka kubutar da mahaifin dan kwallon, suna Michael Obi daga wadanda ke garkuwa da shi a dajin Egede Udi da ke jihar Enugu.

Sanawar ta kara da cewar ranar 29 ga watan Yuni ne dai aka sace mahaifin dan wasan a tsakanin jihohin Benue da Enugu a lokacin da zai je kudu maso gabashin Najeriyar daga garin Jos.
Sai dai ba a samu labarin sace shin ba har sai bayan da aka sako shi a ranar Talata.
Bayan masu garkuwa da mutanen sun ka kama Mista Obi da direbansa sun shiga da su wani daji, kuma suka fara neman naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa, a cewar sanarwar.

Amma da jami'an 'yan sanda suka samu bayanai game da wurin da suke, sai suka afka wa mutanen.

Bayan an yi bata-kashi na wani lokaci sai masu garkuwa da mutanen suka tsere, suka bar Mista Obi da direbansa, in ji sanarwar.

Ko a shekarar 2011 ma an sace mahaifin na Mikel Obi, kuma aka kubutar da shi daga bisani.

Garkuwa da mutane dai wani laifi ne da ake ci gaba da gani duk da cewa jami'an tsaro sun ce suna iya kokarinsu don dakile matsalar.
bbchausa.
An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.

July 02, 2018

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.

Sananniyar 'yar jaridar nan me yawan jawo cece-kuce kuma diya a gurin tsohon gwamnan jihar Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana sha'awarta da shiga addinin musulunci, tace babu abinda addinin kiristanci da take kanshi a yanzu ya jawo mata banda dimuwa da rudani.
Kemi ta bayyana hakane a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada Zumunta da muhawara inda ta sanya hotunan ta sanye da Hijabi sannan ta rubuta cewa:
Kwanannan zata karbi addinin musulunci, kuma a da ta kasance tare da kakarta wadda ta rasu tana da shekaru dari da biyu a Duniya, makarantar da take zuwa kusa da gidan kakartane shi yasa ta koma can da zama, su kanyi sallah sau biyar a rana ba sau daya a sati ba kamar yanda take yi tare da shaidanun mutane yanzu ba, tace, suna shagulgulan sallah babba da karama tare.
Tace Musulunci addinine na zama lafiya kuma a cikinshine zata samu nutsuwa.
Ta dai karkare zancenta da cewa, yanzu babu ruwanta da addinin kiristanci, dan kuwa babu abinda ya tsinana mata a rayuwa banda rudani, musulunci zata koma kuma duk wanda baya son addinin musulunci sai ya dena bibiyarta da lamurranta, komai yana da lokaci dama, yanzu dai ta tabbata cewa a addinin musuluncine zata samu nutsuwar da take nema.
Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo. Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo. Reviewed by Ibrahim Auwal on July 02, 2018 Rating: 5
Powered by Blogger.