An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi


Rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta ce ta yi nasarar kubutar da mahaifin kyaftin din Super Eagles ta Najeriya, Mikel Obi, kwana uku bayan an sace shi.

Wata sanarwar da kakakin rundunar, SP Ebere Amaraizu, ya fitar ta ce da sanyin safiyar Litini ne jami'an 'yan sandan suka kubutar da mahaifin dan kwallon, suna Michael Obi daga wadanda ke garkuwa da shi a dajin Egede Udi da ke jihar Enugu.

Sanawar ta kara da cewar ranar 29 ga watan Yuni ne dai aka sace mahaifin dan wasan a tsakanin jihohin Benue da Enugu a lokacin da zai je kudu maso gabashin Najeriyar daga garin Jos.
Sai dai ba a samu labarin sace shin ba har sai bayan da aka sako shi a ranar Talata.
Bayan masu garkuwa da mutanen sun ka kama Mista Obi da direbansa sun shiga da su wani daji, kuma suka fara neman naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa, a cewar sanarwar.

Amma da jami'an 'yan sanda suka samu bayanai game da wurin da suke, sai suka afka wa mutanen.

Bayan an yi bata-kashi na wani lokaci sai masu garkuwa da mutanen suka tsere, suka bar Mista Obi da direbansa, in ji sanarwar.

Ko a shekarar 2011 ma an sace mahaifin na Mikel Obi, kuma aka kubutar da shi daga bisani.

Garkuwa da mutane dai wani laifi ne da ake ci gaba da gani duk da cewa jami'an tsaro sun ce suna iya kokarinsu don dakile matsalar.
bbchausa.
An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi An kubutar da mahaifin Mikel Obi bayan sace shi Reviewed by Ibrahim Auwal on July 04, 2018 Rating: 5

No comments:

Anan zaka rubuta tsokacinka

Powered by Blogger.